20 Oktoba 2016 - 11:13
Putin Da Assad Sun Tattauna Kan Rikicin Syria Da Kuma Yaki Da Ta'addanci

Shugabannin kasashen Rasha da Syria sun gudanar da wata tattaunawa a jiya ta wayar taroho, dangane da halin da ake ciki a Syria da kuma batun ci gaba da yaki da ta'addanci a kasar.

Tashar talabijin ta Alalam ta bayar da rahoton cewa, shugaba Putin na Rasha ya tuntubi takwaransa na Syria Bashar Assad a jiya ta wayar tarho, inda suka tattauna dangane da halin da ake ciki a rikicin da aka haifar a kasar ta Syria, da kuma hanyoyin da ake bi domin kawo karshen lamarin, tare da jaddawar dukkanin bangarorin biyu kan ci gaba da yin aiki tare wajen yaki da ta'addanci a kasar.

Assad ya jinjina wa Rasha, dangane da tsayin dakan da ta yi wajen mara baya ga kasar Syria a yakin da take yi da kungiyoyin 'yan ta'adda, da ke samun goyon baya da dauki daga manyan kasashen duniya da kuma wasu daga cikin kasashen larabawa da suke da sabanin siyasa da Syria, yayin da Putin ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da mara baya ga Syria har sai an ga bayan ta'addanci a kasar.288